logo

HAUSA

Shuagaban Namibia ya taya ‘yar wasan kasar murnar samun lambar Azurfa a wasannin Olympics

2021-08-04 14:05:29 CRI

Shuagaban Namibia ya taya ‘yar wasan kasar murnar samun lambar Azurfa a wasannin Olympics_fororder_OIF-C

Shugaban Namibia Hage Geingob, ya taya ‘yar wasan kasar Christine Mboma murna, bisa nasarar da ta samu a tseren mita 200 ta mata a wasan karshe na wasannin Olympics na birnin Tokyo.

Christine Mboma ‘yar shekara 18 ta samu lambar Azurfa ne bayan ta zo a matsayin na biyu, bayan Elaine Thompson-Herah ‘yar kasar Jamaica, yayin da wata ‘yar Namibia Beatrice Masilinga, ta zo a matsayi na 6. (Fa’iza Mustapha)