logo

HAUSA

An Kunna Filitar Gasar Wasannin Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Beijing Ta Shekarar 2022 A Tsohuwar Olympia

2021-10-18 19:27:00 CRI

A yau ne, aka kunna wutar gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ta shekarar 2022 a wurin da aka kirkiro wasannin a tsohuwar Olympia dake kasar Girka.

A lokacin bikin gargajiya, 'yar wasan kwaikwayo Xanthi Georgiou wadda ta fito a matsayin tsohuwar babbar fada ta Girka, ta yi amfani da madubi don mai da hankali kan hasken rana da kunna fitila a gaban wurin bauta na Hera mai shekaru 2,500 a tarihin Girkanci.

Shugaban kwamitin kula da harkokin wasannin Olympic na kasa da kasa (IOC) Thomas Bach ya ce, “Beijing zai rubuta tarihi a matsayin birni na farko, da ya taba karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin zafi a shekarar 2008 da ta lokacin hunturu. Gasar wasannin Olympics ta lokacin huturu da Beijing zai karbi bakunci a shekarar 2022, za ta hada Sinawa da mutanen sauran sassan duniya, za kuma ta gabatar da hangen nesa na kasar Sin na shigar da mutane miliyan 300 cikin wasannin dusar kankara da na kankara, tare da sauya wasannin lokacin hunturu har abada. Kuma duniya za ta ga wannan gasa mai ban sha’awa, da kasar ke maraba da 'yan wasan da su halarci gasar ta lokacin hunturu.”

A karshen bikin, babbar fadar za ta mika wutar ga dan wasan gudun kankara mai taushi na Girka, Ioannis Antoniou, a cikin filin wasan da ya fara karbar bakuncin gasar wasannin a daruruwan shekaru da suka wuce.

Jimillar masu rike da fitilar gasar guda uku ne, za su mika fitilar a tsohuwar Olympia. Tsohon dan wasan tseren kankarar kasar Sin mai saurin gudu Li Jiajun shi ne na biyu.

Bayan wata gajeriyar tattaki na mika fitilar, za a mayar da fitilar zuwa Athens, inda gobe Talata za a mika ta ga masu shirya gasar da za a gudanar a Beijing a shekarar 2022.

Za a gudanar da gasar wasannin Olympics na hunturu na XXIV daga ranar 4 zuwa 20 ga watan Fabrairun shekarar 2022, sai kuma gasar ajin nakasassu wato Paralympics ta biyo baya.(Ibrahim)

Ibrahim