logo

HAUSA

Kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar sun taya tawagar kasar a gasar wasannin Olympics murna

2021-08-08 20:37:46 CRI

Kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar Sin, sun aike da sakon taya murna ga tawagar kasar a gasar wasannin Olympics ta Tokyo.

Tawagar kasar Sin ta kammala dukkan gasanninta a Tokyo a yau Lahadi, inda ta lashe lambobin Zinare 38 da ta Azurfa 32 sai Tagulla 18. Tawagar ita ce ta zo ta biyu bayan Amurka, a yawan lambobin yabo. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha