logo

HAUSA

Tokyo: Ya Kamata A Cimma Daidaito Kan Kara Hada Kai

2021-08-09 21:28:14 CRI

Jiya Lahadi da dare ne aka rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi karo na 32 a birnin Tokyo, hedkwatar kasar Japan, inda shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa Thomas Bach ya ce, gasar da aka yi a wannan karo, ita ce ta fi fuskantar kalubale, wadda ba a taba gani a baya ba, gasar da ta karfafa zukatan mutane a sassa daban daban na duniya da kara imaninsu kan makomar gasar.

Mista Bach ya fadi gaskiya. Sakamakon barkewar annobar COVID-19, ya sa aka dakatar da gudanar da gasar na tsawon shekara guda, wadda kuma aka gudanar a filayen wasa, ba tare da ‘yan kallo ba. Haka kuma, ita ce gasar wasannin Olympics ta farko bayan da aka tanadi “kara hadin kai” cikin kundin tsarin Olympics, lamarin da ya sa gasar da aka yi a Tokyo ta sha bamban sosai, wadda kuma ta ba mutane mamaki, tare da sanya mutane kara tunani sosai.

Ko da yake barkewar annobar ta yi illa ga tunani da jikin ‘yan wasa da aikin horaswarsu, amma a karshe dai sun samu nasarar daidaita matsaloli, sun nuna kwarewarsu, sun kalubalanci kansu don samun ci gaba, sun kuma karya matsayin bajimta a wasu wasanni, a kokarin kyautata kansu yayin da suke daidaita matsaloli. A cikin jerin sunayen kasashe da yankuna da suka lashe lambobin yabo a gasar, kungiyoyin ‘yan wasa guda 65 ne suka samu lambobin zinariya, yayin da wasu kungiyoyin ‘yan wasa 93 suka samu lambobin yabo, lamarin da ya nuna kyautatuwar matsayin wasannin motsa jiki a duniya.

Har ila yau, a gabannin bude gasar, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa ya tanadi “kara hadin kai” cikin kundin tsarin Olympics, lamarin da ya kara sabon abu cikin ruhin Olympics. Hakika dai, hadin gwiwar da aka nuna a wasannin motsa jiki tana da matukar muhimmanci wajen tinkarar kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu. Babu wanda zai iya yaki da annobar ta COVID-19, kara azama kan farfadowar tattalin arzikin duniya, da daidaita sauyin yanayi shi kadai. Akwai bukatar kowa da kowa ya cimma ra’ayi daya duk da bambance-bambance da ke akwai a tsakaninsu, su kuma hada kansu sosai. Wannan shi ne yadda ruhun wasannin Olympics na zamani ke kara azama kan ci gaban zamantakewar al’ummar dan Adam, wato sa kaimi kan samun jituwa tsakanin mutane, a kokarin raya duniya da kowa zai ji dadin zama a cikinta. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan