logo

HAUSA

Kara Azama Kan Kiyaye Rawayan Kogi Ya Nuna Aniyar Kasar Sin Ta Raya Kanta Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

2021-10-23 20:30:26 CRI

Kwanan baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi rangadin aiki a lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin, tare da jagorantar taron bita kan kara azama kan kiyaye muhallin halittu a yankin rawayan kogi da samun ci gaba mai inganci. Shugaba Xi ya jaddada cewa, aiwatar da ayyukan kiyaye rawayan kogi yadda ya kamata, babban aiki ne na kasar Sin. Wajibi ne a tabbatar da samun babban ci gaba a fannonin kiyaye muhallin halittu a yankin rawayan kogi da samun bunkasuwa mai inganci yayin da kasar Sin take aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14. Lamarin da ya nuna aniyar kasar Sin ta bin hanyar raya kasa ta zamani ba tare da gurbata muhalli ba, inda take ba da fifiko kan kiyaye muhallin halittu.

A ‘yan kwanakin baya, kasar Sin ta karbi bakuncin shirya taron kolin shugabanni na babban taron kasashen da suka daddale yarjejeniyar kiyaye kasancewar halittu daban daban a duniya karo na 15, inda shugaba Xi Jinping ya yi karin bayani kan muhimmancin zaman tare tsakanin dan Adam da muhalli cikin jituwa, tare da jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye muhallin halittu, ya kuma yi kira ga sassa daban daban da su gaggauta fito da hanyar ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kara azama kan samun bunkasar tattalin arziki da kuma kiyaye muhalli tare, da kafa duniyarmu mai ci gaban tattalin arziki da kyakkyawan muhalli. A yayin da ya yi rangadin aiki a lardin Shandong kuma, shugaba Xi ya gabatar da sabbin bukatu kan kiyaye rawayan kogi da samun ci gaba mai inganci, lalle kasar Sin ta cika alkawarinta na daukar hakikanin matakan kiyaye muhallin halittu.

Kamar yadda madam Dechen Tsering, darektar ofishin hukumar tsara shiri kan muhalli ta MDD a yankin Asiya da tekun Pasifik ta fada a kwanan baya, kasar Sin tana jagorantar aikin kiyaye muhalli a duniya. Tana taka muhimmiyar rawa a fannonin daidaita sauyin yanayi, dakatar da gurbata muhalli da kiyaye kasancewar halittu daban daban a duniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan