logo

HAUSA

Sin: Amurka da Burtaniya ba su damu da hakkin dan Adam da 'yanci a Hong Kong ba

2021-10-22 20:22:34 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a Jumma’ar nan cewa, shin da gaskiya ne cewa, Amurka da Burtaniya sun damu da batun hakkoki da ‘yancin jama’ar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin? Amma gaskiyar magana shi ne, suna kawo cikas ga doka a yankin, tare da neman tayar da husuma.

A jiya ne, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da wata sanarwa da ke nuna damuwa game wai yadda ake "ci gaba da take" 'yancin dan Adam da na walwala a Hong Kong. A wannan rana, sakataren harkokin wajen Burtaniya, ya bayyana cewa, shawarar da yankin ya yanke ta soke wakilcin wasu kansilolin gundumomi a Hong Kong tana da matukar damuwa.

Da yake mayar da martani kan wannan batu, Wang Wenbin ya ce matakin da gwamnatin yankin musamman na Hong Kong ya dauka game da cancantar ma’aikatan da suka dace a matsayin kansilolin gunduma, ya yi daidai da muhimmiyar dokar yankin da ka’idoji masu ruwa da tsaki na yankin, kuma babu tababa a kai. Hong Kong, wani bangare ne na kasar Sin, kuma al'amuran Hong Kong, harkokin cikin gidan kasar Sin ne. Babu wata kasar waje da ke da hakkin sukar lamurran Hong Kong da harkokin cikin gida na kasar Sin. (Ibrahim)

Ibrahim