logo

HAUSA

Xi’an: An Kaddamar Da Wasannin Nakasassu Na Kasar Sin Karo Na 11 Da Wasannin Olympics Na Musamman Karo Na 8

2021-10-23 16:33:36 CRI

Xi’an: An Kaddamar Da Wasannin Nakasassu Na Kasar Sin Karo Na 11 Da Wasannin Olympics Na Musamman Karo Na 8_fororder_wasanni

An kaddamar da gasar wasannin motsa jiki na nakasassu karo na 11 da gasar wasannin Olympics na musammam karo na 8 na kasar Sin, jiya Jumma’a a birnin Xi’an na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar.

Wannan ne karon farko da wasannin 2, wadanda za su gudana daga ranar 22 zuwa 29 ga watan Oktoba, za su gudana a lardi guda, kuma a shekara guda da aka gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin, wadda aka kammala karo na 14 a ranar 27 ga watan Satumba.

A jiya Jumma’a da dare ne mataimakiyar firaministan kasar Sin, Sun Chunlan, ta sanar da kaddamar da wasannin biyu a hukumance, yayin wani gaggarumin biki da ya gudana a cibiyar wasanni ta birnin Xi’an.

Katafaren bikin ya samu halartar ‘yan wasa nakasassu 4,484 da za su fafata a wasanni 43, wadanda suka hada da irin na lokacin zafi da na hunturu da na tsakanin al’umma.

Kungiyoyi 35 ta ‘yan wasan, na wakiltar larduna, da manyan biranen da ke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya kai tsaye, da yankuna masu cin gashin kansu, da yankunan musammam na Hong Kong da Macao. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha