logo

HAUSA

MOC: Ana Sa Ran Jarin Waje A Kasar Sin Zai Zarce Yuan Triliyan 1 A Bana

2021-10-23 15:59:37 CRI

Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin wato MOC, ta ce kasar na sa ran kara jawo jarin waje da zai kai sama da kudin Sin RMB yuan triliyan 1 daga ketare a shekarar bana.

Yayin wani taron manema labarai, shugaban sashen kula da jarin waje na ma’aikatar Zong Changqing, ya ce a bangaren dalar Amurka, an yi hasashen jarin ketare a kasar Sin zai zarce dalar Amurka biliyan 160 a bana.

Yayin da yake yabawa da yanayin jarin ketare a kasar Sin, wanda ya zarce yadda ake tsammani tun daga farkon bana, Zong ya ce har yanzu, Sin na fuskantar kalubale masu tsanani bisa la’akari da barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, da sauyawar tsarin samar da kayayyaki a duniya da sauran wasu batutuwan da ba na kudi ba, ciki har da kafa shingaye.

Ya kuma bayyana cewa, ci gaba da farfadowar tattalin arziki da babbar kasuwa da cikakken tsarin masana’antu da isassun ma’aikata da ingantattun ababen more rayuwa, za su taimakawa kasar Sin wajen kara jan hankalin masu zuba jari na kasashen ketare.

Wani nazari na baya-bayan nan da ma’aikatar MOC ta yi kan manyan kamfanonin ketare 3,000 dake kasar Sin, ya nuna cewa, kaso 93.3 na kamfanonin na da kyakkyawan fata kan ci gabansu a kasar Sin.

Har ila yau daga cikin kamfanonin, kaso 99 sun ce ba su da shirin rage jarinsu ko janyewa daga kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha