logo

HAUSA

Kenya ta bukaci a mayar da hankali kan masu yawon bude ido na cikin gida domin farfado da bangaren

2021-09-28 11:40:30 CRI

Kenya ta bukaci a mayar da hankali kan masu yawon bude ido na cikin gida domin farfado da bangaren_fororder_210928-Kenya urges tourism sector to focus on domestic travelers to revive industry-f03

Kenya ta bukaci masu ruwa da tsaki a bangaren yawon bude ido na kasar, su mayar da hankali kan matafiya na cikin gida domin farfado da bangaren dake fuskantar tasirin dakatar da tafiye-tafiye tsakanin kasa da kasa da aka yi, da nufin dakile annobar COVID-19.

Babbar sakatariyar ma’aikatar kula da yawon bude ido ta kasar Safina Kwekwe, ta ce masu yawon bude ido na cikin gida za su iya farfado da harkokin yawon bude ido a kasar, yayin da ake fama da annobar COVID-19 da ta kawo tsaiko ga harkokin kasuwanci a fadin duniya.

Ta kara da cewa, bangaren na bada gagarumar gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar. Tana mai cewa, yawon bude ido a cikin gida, zai ceto bangaren daga durkushewa. (Fa’iza Mustapha)