logo

HAUSA

Madatsar ruwa ta Thwake dake Kenya ta ingiza bunkasuwar tattalin arziki da al’ummar kasar

2021-09-13 13:05:52 CRI

Afrika wani muhimmin bangare ne na hadin kan kasa da kasa game da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Wasu manyan ababen more rayuwa ciki hadda layin dogo, da hanyoyin mota, da filayen jiragen sama, da tasoshin jiragen ruwa, da madatsar ruwa da sauransu sun taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin Afrika da al’ummar kasashen. Daga cikinsu saurin bunkasuwar makamashi mai tsabta ya ba da taimako wajen raya shawarar “ziri daya da hanya daya” mai kiyaye muhalli.

Madatsar Thwake dake kan mahadar kogin Thwake da Athi, aiki mafi girma na albarkatun ruwa, wanda kamfanin GE ZHOU BA na kasar Sin ya ba da taimako gina shi.

Faith Nazbi wata kwararriya ce a fannin kiyaye muhallin hallitu, tana kula da aikin sa ido kan yadda ake aiwatar da manufofin kiyaye muhalli. Gidanta yana kusa da madatsar, ta ce garinsu yana fama da fari, ana dogaro da hasken rana don samar da wutar lantarki, hakan ya sa ana fuskantar karancin isashen wutar lantarki. A ganinta, wannan aiki ya samar da dimbin guraben aikin yi kuma ya canja fuskar garinta, Ta ce: 

“Madatsar ruwan ta kawo amfani ga mutane da dama, ciki har da ingiza ayyukan tattalin arzikin wurin. Za mu samu isashen ruwan sha da abinci. Hakan ya sa, a ganina wannan aiki zai kawo amfani matuka ga al’ummar wurin. Za mu iya yin zaman rayuwa mai kyau bisa dogaro da shi.” (Amina Xu)