logo

HAUSA

Babban sakataren jam’iyya mai mulkin Kenya: Batun rahoton asalin COVID-19 na Amurka siyasa ce ba tsarin kimiyya ba

2021-09-08 10:37:34 CRI

A kwanan nan, rahoton binciken asalin cutar COVID-19, wanda hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ta fitar ya yi matukar jan hankalin dukkan bangarori. Sai dai Raphael Tuju, sakatare-janar na jam’iyya Jubilee mai mulkin kasar Kenya, ya bayyana a wata hira da wakilin babban gidan radiyo da talabijin na kasar Sin CMG cewa, rahoton da Amurka ke ikirarinsa ba shi da ma’ana, kuma bai dace da tsarin kimiyya ba, asali ma manufa ce ta siyasa kuma ba zai taimaka wajen yaki da cutar COVID-19 ko kuma sauran annoba da za su iya yaduwa a nan gaba ba.

Tuju ya ce, kasar Sin ta samar da riga-kafi, da kayayyakin kiwon lafiya da sauran tallafi wanda ta baiwa kasashen duniya ciki har da kasar Kenya kuma ta yi musayar kwarewar da ta samu a yaki da annobar, wanda shi ne hakikanin abin da Kenya ke bukata. (Ahmad)