logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Tuntubi Amurka A Hukumance Kan Batun Hong Kong

2021-08-08 21:04:19 CRI

Kasar Sin Ta Tuntubi Amurka A Hukumance Kan Batun Hong Kong_fororder_hong kong

Yau Lahadi madam Hua Chunying, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta amsa tambayar manema labaru dangane da takardar bayani da shugaban Amurka ya sa hannu a kai kan batun Hong Kong.

Madam Hua ta yi nuni da cewa, takardar bayanin ya bata sunan dokar tsaron kasa a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin da kuma manufofin kasar Sin na tafiyar da harkokin Hong Kong, lamarin da ya sake shaida yadda Amurka ke tsoma baki cikin harkokin Hong Kong da harkokin cikin gidan kasar Sin. Ta ce kasar Sin na adawa da hakan tare da nuna rashin jin dadinta, kuma ta riga ta tuntubi Amurka a hukumance.

Kakakin ta kara da cewa, tsarawa da kuma aiwatar da dokar tsaron kasa a Hong Kong sun kyautata yadda ake tafiyar da harkoki bisa doka a Hong Kong, sun kuma dawo da tsaro da kwanciyar hankali a yankin, tare da kiyaye halaltattun hakkokin mazauna. A cewarta, bayanin Amurka na wai samar wa mazauna Hong Kong mafaka, ba shi da kan gado. Ta ce ainihin nufin Amurka shi ne, goyon bayan masu adawa da gwamnatin tsakiyar kasar Sin wadanda ke yunkurin ta da kura a Hong Kong, da illata wadata da kwanciyar hankali a yankin, a yunkurin hana ci gaban kasar Sin。(Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan