logo

HAUSA

Takunkumin ban dariya da Amurka ta dauka kan Hong Kong zai haifar da sakamako ne sabanin yadda ake tsammani

2021-07-17 20:44:27 cri

Takunkumin ban dariya da Amurka ta dauka kan Hong Kong zai haifar da sakamako ne sabanin yadda ake tsammani_fororder_微信图片_20210717203032

Jiya Jumma’a, kasar Amurka ta ba da sanarwar da ake kira wai "gargadi a fannin kasuwanci" game da yankin Hong Kong na kasar Sin, inda ta bata sunan yanayin kasuwancin Hong Kong da sanya takunkumi ga jami'an hukumomin gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake yankin. Dangane da tabbacin halin da yankin Hong Kong ke ciki, Amurka ta sake tsokano wani harin rashin hankali amma mai kuzari.

A tsakiyar shekarar da ta gabata, bayan aiwatar da Dokar Tsaron Kasa ta Hong Kong, sai Amurka ta sanar da cewa, ba za ta ba Hong Kong kulawa ta musamman ba. Amma sakamakon shi ne, idan aka kwatanta da watanni 12 kafin aiwatar da dokar, yawan kudin da aka samu daga sabbin hannayen jarin da aka zuba a Hong Kong cikin shekara daya da ta wuce ya zarce dalar Hong Kong biliyan 500, wanda ya karu da kimanin 50% bisa na da. Kana jimillar kudaden bankunan Hong Kong ya karu da 5.6%, adadin da ya kai dalar Hong Kong tiriliyan 14.9. Dokar Tsaron Kasa ta Hong Kong ta bai wa masu saka jari na kasashen duniya kwarin gwiwa. Rahoton da Asusun Ba da Lamuni na Duniya ya bayar a kwanakin baya, ya sake tabbatar da matsayin Hong Kong na cibiyar hada-hadar kudi ta duniya.

Kwanan nan, wasu kafofin yada labarai sun ruwaito cewa, ‘yan kasuwar Amurka a Hong Kong gaba daya suna adawa da sanarwra "gargadi a fannin kasuwanci" da kasarsu ta kaddamar. Rob Chipman, babban Daraktan Kamfanin Kula da Sufuri na Kasa da Kasa na Asian Tigers, wanda ya zauna a Hong Kong na tsawon shekaru 35, ya bayyana “mamaki da bacin rai” game da wannan “gargadi a fannin kasuwanci”. Tara Joseph, shugabar kungiyar 'yan kasuwar Amurka a Hong Kong, wacce ke da kamfanoni mambobin 1,400, ta ce mambobinta “har yanzu suna ganin darajar Hong Kong.”

Ya kamata a san cewa, dalilan da suka sa Hong Kong ke jan hankalin masu saka hannun jari na duniya su ne yanayinsa na kebabben wurin, tsarin kasuwancinsa, da kwararru da dai sauransu, wadanda kuma ba Amurka ce ta ba shi ba. Bisa ingantuwar “Shirin shekaru 5 karo na 14” na kasar Sin, musamman yadda ake raya yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macao, za a kara saurin sanya Hong Kong cikin tsarin ci gaban kasar Sin bisa manyan tsare-tsare. (Bilkisu Xin)