logo

HAUSA

Sin Ta Ce Yunkurin Shisshigin Kasashen Waje A Harkokin Cikin Gidan Hong Kong Tamkar Daukar Dala Ba Gammo Ne

2021-07-18 17:42:39 CRI

Sin Ta Ce Yunkurin Shisshigin Kasashen Waje A Harkokin Cikin Gidan Hong Kong Tamkar Daukar Dala Ba Gammo Ne_fororder_hong kong

Kasar Sin ta bukaci kasar Amurka da ta gaggauta daina yin shisshigi a harkokin yankin Hong Kong, wanda batu ne dake shafar harkokin cikin gidan kasar Sin, kana bangaren kasar Sin zai dauki dukkan matakan da suka dace bisa doka domin kare ikon mulkin kan kasa da tsaron kasa, gami da ci gaban moriyar kasa, in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar jiya Asabar 17 ga wata.

Kakakin ya yi wannan tsokaci ne bayan da gwamnatin kasar Amurka ta fidda wata sanarwa da ta kira wai da sunan “shawarar kasuwanci ta Hong Kong", kana ta sanya takunkumai kan wasu jami’ai 7 na ofishin gwamnatin tsakiya dake yankin musamman na Hong Kong (SAR).

Hong Kong, bangare ne na kasar Sin, kuma harkokin Hong Kong sun kasance harkokin cikin gidan kasar Sin ne, kamar yadda kakakin ya bayyana cikin wata sanarwa. Bugu da kari, duk wani matsin lamba daga waje dake yunkuri yin shisshigi a harkokin Hong Kong za su tsinci kansu ne tamkar abin da nan ne da ake cewa “daukar Dala ne babu gammo."

Sanarwar ta ce, kasar Sin tana aiwatar da manufar “kasa daya, amma tsarin mulki biyu", inda al’ummar Hong Kong suke iya gudanar da harkokin dake shafar yankin na Hong Kong da kansu. Sanarwar ta jaddada cewa, tun bayan aiwatar da dokar tabbatar da tsaron kasa a yankin musamman na Hong Kong, ana ci gaba da samun kwanciyar hankali a Hong Kong, inda ake kuma samun ingantuwar doka da oda, da kara farfadowar yankin.

Rahotannin kafofin yada labaru na baya bayan nan sun nuna cewa, ana kara yin watsi da wannan shawarar kasuwanci da gwamnatin Amurka ta fitar a tsakanin ‘yan kasuwar Amurka dake Hong Kong, a cewar kakakin.

Sai dai kuma duk da hakan, gwamnatinn Amurka, ta rufe idonta da gangan don kaucewa gaskiya tare da toshe kunnuwanta don kin sauraron kiraye kirayen ‘yan kasuwar, a maimakon hakan, tana yunkurin yin amfani da wannan shawarar kasuwanci wajen dakile kyakkyawar makomar yankin Hong Kong da cin zarafin masu zuba jari na kasashen waje a yankin Hong Kong.

A cewar kakakin, wannan batu ya kara fito fili da mummunar aniyar Amurka na yunkurin lalata zaman lafiya da ci gaban yankin Hong Kong, tare da yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin, da neman gurgunta ci gaban kasar Sin.(Ahmad)

Ahmad