logo

HAUSA

Amurka Na Yunkurin Haddasa Tashe-tashen Hankula A Hong Kong

2021-09-24 20:18:17 CRI

Yau Jumma’a ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata takarda kan yadda kasar Amurka ta tsoma baki a cikin harkokin yankin Hong Kong na kasar Sin, da nuna goyon baya ga masu tayar da tarzoma a yankin.

A cikin wannan takarda, kasar Sin ta yi karin bayani kan miyagun ayyukan da Amurka ta yi daga shekarar 2019, a yunkurin haddasa tashin hankali a Hong Kong. Takardar mai kunshe da babi guda 5 ta gabatar da abubuwa 102 da Amurka ta yi, ciki had da kirkiro shirin doka kan Hong Kong, sanya takunkumi babu wani dalili, shafa bakin fenti kan harkokin Hong Kong, ba da mafaka da goyon bayan masu tayar da tarzoma a yankin, hada kai da kawayenta don tsoma baki cikin harkokin Hong Kong da dai sauransu. Kowa ya fahimci yadda Amurka take kokarin goyon bayan masu tayar da tarzoma a Hong Kong ba tare da wani kunya ba. Kuma Amurka ta tsara wasu dabaru don shafa kashin kaji kan yadda gwamnatin Sin take tafiyar da harkokin Hong Kong.

Sinawa ba sa son yin fada da kowa, amma ba sa jin tsoron fada idan aka nemi kai su makura da gangan. Yunkurin Amurka na hana ci gaban kasar Sin ta hanyar ta da tarzoma a Hong Kong, ba zai yi nasara ba. Kasar Sin ta mayar da nata martani kan Amurka, alal misali, sanya takunkumi kan daidaikun Amurkawa da hukumominta, fitar da dokar nuna adawa da takunkumin kasashen waje, da gabatar da takardar a yau. Dukkan matakai masu dacewa da kasar Sin ta dauka sun nuna cewa, ya zama tilas Sin ta mayar da martanin da ya wajaba kan dukkan matakai da bayanai na tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta, da barnata moriya da mutuncin kasarta.

Yanzu kura ta kwanta a Hong Kong. Sakamakon jerin zabukan da aka yi a Hong Kong, ya sa an aiwatar da ka’idar “masu kishin Hong Kong na tafiyar da harkokin yankin”, kana an rika kyautata manufar “kasa daya amma tsarin mulkin biyu”, ta yadda za a samu dawamammen kwanciyar hankali a Hong Kong. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan