logo

HAUSA

Amurka Wadda Ke Kokarin Nuna Karfin Soja Tana Addabar Duniya Sosai

2021-10-21 20:57:42 CRI

Kwanan baya, wasu manyan jami’an Amurka sun sake yayata batun wai, kasar Sin barazana ce. Lalle Amurka mai karfi a duniya, wadda ke himmatuwa wajen raya aikin soja, tare da sha’awar nuna karfin soja ta ayyana wata kasa ta daban a matsayin barazana. Gwano ba ya jin warin jikinsa. Nufinta shi ne neman hujjar inganta karfin soja da ci gaba da yin danniya a duniya.

Yau wata guda ke nan, majalisar wakilan Amurka ta zartas da shirin dokar kasafin kudi ta fuskar aikin soja a shekarar 2022, inda aka ware dalar Amurka biliyan 770 ga ma’aikatar tsaron kasar. Haka kuma za a yi amfani da dalar Amurka biliyan 28 daga cikin kudin kan shirin makaman nukiliya karkashin shugabancin ma’aikatar makamashin Amurka. Sanin kowa ne cewa, Amurka tana da wurin adana makaman nukiliya mafi ci gaba da girma a duniya. Amma yanzu za ta kara zuba makudan kudade don kara karfinta na makaman nukiliya daga dukkan fannoni, lamarin da ya sanya kasashen duniya kara nuna damuwa.

Ban da haka kuma, kasashen Amurka, Birtaniya da Australiya sun sanar da kafa huldar abokantaka ta tsaro a tsakanin kasashen 3 wato AUKUS, tare da daddale yarjejeniyar yin amfani da fasahar jirgin karkashin ruwa na yaki dake aiki da karfin nukiliya tsakanin su da kera jirgin. Idan an aiwatar da yarjejeniyar, to, hakan na iya illata daidaito a yankin Asiya da tekun Pasifik bisa manyan tsare-tsare, kana yankin zai fuskanci barazana a fannoni da dama.

Abin da Amurka ta yi ya sanya duniya fahimtar cewa, Amurka tana matukar sha’awar aikin soja ne, domin za ta samu babbar moriya daga yake-yake, sa’an nan za ta yi amfani da kudaden wajen daukar matakin soja a kusan dukkan nahiyoyi 5 a duniya, a yunkurin ci gaba da yin danniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan