logo

HAUSA

Sin: Amurka tana ikirarin Sin ta tsaurara matakan kera makamai ne don neman karkatar da hankalin duniya

2021-10-19 20:26:44 CRI

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya shaidawa taron manema labarai Talatar nan cewa, ikirarin da Amurka ke yi na cewa, wai Sin na kara karfin tseren mallakar makamai, ba komai ba ne illa zargi da neman karkatar da hankalin duniya.

Wang Wenbin ya ce, kasar Sin tana adawa da ci gaba da wuce gona da iri kan dabarar Amurka ta mayar da “Sin a matsayin barazana” da take yi. Amurka ba wai kawai tana da manyan makaman nukiliya mafi girma da ci gaba a duniya ba, har ma ta zuba tiriliyoyin daloli, don kara karfin nukiliyarta. Yadda Amurka ke kara ruruta "dabarar mayar da kasar Sin a matsayin barazana" ba wani abu ba ne, illa wani uzuri na fadada ikon sojinta da neman cikakken fifiko na tsaro. (Ibrahim)

Ibrahim