logo

HAUSA

Kasar Sin za ta yi maraba da dage haraji kan wasu kayayyakin kasar da Amurka za ta yi

2021-10-21 19:40:14 CRI

Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin (MOC) Alhamis din nan ta bayyana cewa, kasar Sin za ta yi maraba da matakin da Amurka za ta dauka na dage haraji kan wasu kayayyakin kasar Sin.

Mai magana da yawun ma'aikatar Shu Jueting ta bayyana a yayin wani taron manema labarai na yau da kullum cewa, ya kamata Sin da Amurka su yi aiki tare don samar da yanayin da zai kai ga aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci ta bai daya. (Ibrahim)

Ibrahim