Me Ya Sa Aka Jefa Ayaba Dubu 10 A Dab Da Kayan Sassakar Tagulla Mai Siffar Sa A Titin Wall A New York?
2021-10-20 21:29:33 CRI
Kwanan baya, an jefa ayaba dubu 10 a dab da shahararriyar alamar birnin New York na Amurka, wato kayan sassakar tagulla mai siffar sa dake titin Wall, inda kuma aka ajiye wani sabon kayan sassaka mai siffar katon biri a gabansa. Masu shirya harkar sun yi shelar cewa, sun yi hakan ne domin nuna kiyayya kan karuwar gibin da ke tsakanin masu kudi da matalauta a Amurka, da kuma tsarin jari-hujja maras tausayi. Kayan sassaka mai siffar katon biri, alama ce ta talakawa dake gwagwarmaya a ko da yaushe a Amurka. Ayaba dubu 10 sun nuna cewa, titin Wall ya haukace, saboda ma’anar ayaba a Turance wato banana tana nufin hauka.
Yaya gibin da ke tsakanin masu kudi da matalauta a Amurka? Sabbin alkaluman asusun tarayyar Amurka sun nuna cewa, manyan attajiran Amurka da yawansu ya kai kaso 10 cikin dari ne suka mallaki hannayen jari da dukiyar da yawansu ya kai kaso 89 cikin dari a Amurka, lamarin da ya kafa tarihi. Sa’an nan kuma, wannan shi ne karo na farko da yawan dukiyoyin da ke hannun kaso 1 cikin 100 na hamshakan masu kudin Amurka ya wuce jimillar dukiyoyin da ke hannun masu matsakaicin karfi.
Haka zalika jami’ar Havard da sauran hukumomi, sun gabatar da sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a a kwanan baya, inda suka nuna cewa, iyalan da yawansu ya kai kaso 40 cikin dari ne a Amurka suke fama da matsalar tattalin arziki, yayin da kashi 1 cikin kashi 5 ne suka yi asarar kudadensu.
Me ya sa Amurka, wadda kasa ce mafi karfi daya tilo a duniya, ta kau da kai daga kukan fararen hula, tare da barin gibin da ke tsakanin masu kudi da matalauta ya kara karuwa? Kamar yadda rahoton kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD ya bayyana, a kasashe masu kudi, kamar Amurka, masu mulkin kasa suna neman muradun siyasa, wannan ya sa suke barin fararen hula cikin kangin talauci. Idan Amurka ta yi aniyar fitar da jama’arta daga kangin talauci, hakika, za ta samu nasara, amma ba ta da irin wannan aniya. ‘Yan siyasan Amurka suna mulki ne domin samun kudi. Tsirarun kwararru wadanda ke mallakar ikon tattalin arziki da siyasa suna bauta wa kudi ne, a maimakon al’umma. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Amurka Ba Ta Da Hurumin Sukar Xinjiang Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam
- Sin: Amurka tana ikirarin Sin ta tsaurara matakan kera makamai ne don neman karkatar da hankalin duniya
- Sin: Dimokuradiyya ba tsari ne da za a fake da shi ana danniya ba
- Amurka: Amurka Da Sin Za Su Rage Sabani A Tsakaninsu Ta Hanyar Tattaunawa