logo

HAUSA

Sin: Dimokuradiyya ba tsari ne da za a fake da shi ana danniya ba

2021-10-19 20:20:46 CRI

A martanin da ya mayar game da shirin Amurka na karbar bakuncin “taron kolin shugabannin kan dimokuradiyya”, ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, lallai Amurka tana shirya gayyatar kasashen da take ganin suna bin tsarin dimokuradiyya, da nufin raba al’ummomin kasashen duniya cikin rukunin abokan gaba da rukunin abokai bisa tunanin ra’ayin cacar baka.

Da yake mayar da martani kan wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai na yau da kullun Talatar nan cewa, “abin da ministan harkokin wajen Rasha Lavrov ya fada, yana da babbar ma'ana. Dimokuradiyya ba take ba ne, kuma bai kamata a yi amfani da tsari na 'demokuradiyya' don boye matsaloli a cikin ta ba. Mulkin dimokuradiyya ba akida ba ce. Bai kamata mu yi watsi da manyan bambance-bambancen da ke cikin tarihi, da al'adu, da tsarin zamantakewa, da matakan ci gaban kasashe na duniya ba. Haka kuma bai kamata mu yi kokarin mayar da dimokuradiyya kamar ruwan lemon Coca-Cola ba, inda wata kasa daya tilo ke samar da mahadin tsami, kuma duk duniya tana da dandano daya, tana kuma hana kasashe da dama masu 'yanci binciko hanyoyin dimokuradiyya da zai dace da su. Dimokuradiyya ba wata kafa ba ce, ta kakabawa ra’ayi na danniya. Bai kamata mu haifar da rarrabuwar kawuna da fada a duniya karkashin tutar dimokuradiyya ba, da tura duniya zuwa wani zamani mai hadari na yakin cacar baka”.(Ibrahim)

Ibrahim