logo

HAUSA

Amurka: Amurka Da Sin Za Su Rage Sabani A Tsakaninsu Ta Hanyar Tattaunawa

2021-10-08 13:38:55 CRI

Amurka: Amurka Da Sin Za Su Rage Sabani A Tsakaninsu Ta Hanyar Tattaunawa_fororder_sa

Ranar 7 ga wata, a wani taron yin takaitaccen bayani da majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta saba shiryawa, kakakin majalisar Ned Price ya ce, huldar da ke tsakanin Amurka da kasar Sin tana shafar sassa daban daban, tana kuma fuskantar rashin tabbas, yayin da suke takara da juna, suna yi wa juna fito-na-fito, kana suna hada kansu. Amurka na fatan nan gaba za su rage sabani a tsakaninsu ta hanyar tattaunawa yadda ya kamata, a kokarin kara azama kan yin hadin gwiwa a wasu fannoni.

Price ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwar kasashen 2 a fannin sauyin yanayi. Ya kara da cewa, a matsayinsu na kasashe 2 mafiya fitar da hayaki mai dumama yanayi a duniya, sauke nauyi da daukar matakai kan daidaita sauyin yanayi ba kawai domin muradun Amurka da Sin ba, har ma za a karfafa gwiwar sauran kasashen duniya da su dauki matakai. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan