logo

HAUSA

Sin: Nasarorin da kasar Sin ta samu wajen kare hakkokin dan Adam sun ja hankalin duniya

2021-10-18 21:20:07 CRI

A bana ne, ake cika shekaru 30 da wallafa takardar bayanai mai taken “hakkokin dan Adam a kasar Sin”. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a wajen taron manema labarai na yau da kullum a Litinin din cewa, kasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin ci gaban kare hakkin dan Adam na duniya, haka kuma ta ba da babbar gudummawa wajen raya manufar kare hakkin dan Adam ta duniya.

Zhao Lijian ya ce, "Kasar Sin ta kirkiro wata babbar mu'ujiza, ta girmama da kare hakkokin bil-Adama, ta kuma samu nasarar shiga tafarkin ci gaban hakkin dan Adam bisa sigar kasar Sin, kuma ta kawo wa jama'ar Sinawa fa'idodi na zahiri. Rayuwar farin ciki da murmushi na farin ciki na jama'ar Sinawa, shi ne hakkin dan Adam na Sinawa. Yadda Sinawa ke nuna gamsuwa da gwamnatin kasar Sin ya wuce kashi 90% na dogon lokaci. Wannan shi ne martani mafi girma da aka nunawa masu muguwar manufa da masu neman bata sunan kasar Sin dake fakewa da sunan kare hakkin dan Adam.(Ibrahim)

Ibrahim