logo

HAUSA

Sin ta bukaci Japan da ta dakatar da ra’ayi na soji

2021-10-18 20:34:36 CRI

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin cewa, ya kamata kasar Japan ta yi taka tsantsan game da kalamanta da abubuwan da take aikatawa kan batutuwan da suka shafi tarihi, kamar wurin bauta na Yasukuni.

Zhao Lijian ya yi wannan furuci ne, yayin wani taron manema labarai na yau da kullum, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da sadaka na al’ada da firaministan Japan Fumio Kishida ya aika ga wurin bauta na Yasukuni da ake takaddama kansa, don karrama masu laifi na aji-A na Japan da aka yanke wa hukunci a yakin duniya na II, wadda kasashe makwabta ke kallo a matsayin wata alama ta tsohon ra’ayin soja na Japan.

Zhao ya ce, matakin baya-bayan da Japan ta dauka kan batun wurin bauta na Yasukuni, ya sake nuna munanan dabi'unta na tarihin zalunci, kuma kasar Sin ta gabatar da kokenta na musamman ta hanyar diflomasiyya.(Ibrahim)

Tasallah Yuan