logo

HAUSA

Kasar Sin tana goyon bayan IAEA wajen taka rawar da ta dace a fannin kula da dagwalon nukiliya a Fukushima

2021-09-13 19:38:33 cri

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, kasarsa tana goyon bayan Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya wato IAEA a takaice, wajen sauraron cikakkun ra'ayoyin masu ruwa da tsaki bisa iznin da ta samu, da kuma taka rawar da ta dace, wajen kula da dagwalon nukiliya a Fukushima na Japan.

Kakakin ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Litinin, inda ya kuma jaddada cewa, ya kamata Japan ta fuskanci damuwar kasashen duniya, ta soke kudurinta maras dacewa, na fitar da dagwalon nukiliya zuwa teku, kuma ta dakatar da ayyuka daban-daban masu nasaba da hakan.

A cewar kamfanin dillacin labarai na AP, a ranar 9 ga wata, mataimakiyar darakta Janar na hukumar IAEA Lydie Evrard, ta bayyana cewa, rukunin aikin fasaha da hukumar ta kafa, zai kimanta halin tsaro, game da magance dagwalon nukiliya a Fukushima na kasar ta Japan. (Mai fassara: Bilkisu)