logo

HAUSA

Suga Yoshihide ya ce ba zai halarci zaben shugaban jam’iyyar LDP ba

2021-09-03 15:19:47 CMG

Suga Yoshihide ya ce ba zai halarci zaben shugaban jam’iyyar LDP ba_fororder_0903-Japan-Bello2

Firaministan kasar Japan Suga Yoshihide ya bayyana a yau Juma’a cewa, zai mai da cikakken hankali kan aikin tinkarar annobar COVID-19, don haka ba zai halarci zaben shugaban jam’iyyar LDP ta kasar Japan na wannan karo ba.

Wa’adin Yoshihide na aiki a matsayin shugaban jam’iyyar LDP zai cika a karshen wannan wata. An zaci zai yi murabus daga matsayin firaministan kasa zuwa lokacin. (Bello Wang)

Bello