logo

HAUSA

Sin ta koka dangane da ziyarar da ministan tsaron Japan ya kai wurin ibada na Yasukuni

2021-08-14 16:35:20 CRi

Ma’aikatar tsaron kasar Sin, ta bayyana matukar adawa da ziyarar da ministan tsaro Japan, Nobuo Kishi ya kai wurin ibada na Yasukuni, inda kuma ta gabatar da korafinta a hukumance ga kasar.

Kakakin ma’aikatar Wu Qian ne ya bayyana hakan, yayin da yake tsokaci game da ziyarar ta Nobuo Kishi a ranar 13 ga watan Augusta.

Wu Qian, ya ce ziyarar wurin ibada na Yasukuni da ministan tsaron na Japan ya yi, wanda ke girmama mutane 14 da aka samu da aikata manyan laifukan yaki a yakin duniya na II, ya kara bayyana halin rashin kyautawa da Japan ke nunawa dangane da tarihin zaluncinta da niyyarta ta kalubalantar odar duniya bayan yakin.

Kasar Sin na bukatar Japan ta yi nazarin tarihinta na zalunci, ta dauki darasi da gyara kuskurenta, domin samun aminci daga makwabtanta na nahiyar Asiya da ma al’ummun duniya, ta hanyar ayyuka na kwarai.

A cewarsa, a baya-bayan nan, ma’aikatar tsaron Japan ta dauki munanan matakai kan batutuwan da suka shafi kasar Sin, yana mai cewa Japan ta hada kai da kasashen dake wajen nahiyar wajen bata tsarin tsaron kasar Sin da ci gaban rundunarta na soji, inda ta yi wasu atisayen soji da tsoma baki cikin batun Taiwan, wanda batu ne na cikin gidan Sin tare da daukar matakan takala a tekun kudancin Sin.

Bugu da kari, kakakin ya ce, Sin na kira ga Japan da ta yi watsi da tunanin yakin cacar baka, ta hada hannu da Sin, ta hanyar kiyaye tanadin daftarorin siyasa 4 dake tsakanin kasashen, kuma bisa tushen mutunta juna da kaucewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidansu da inganta ci gaban dangantakarsu a fannin tsaro, bisa hanyar da ta dace. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha