Sin ta nuna rashin amincewa da yadda firaministan Japan ya kira Taiwan da kasa mai cin gashin kai
2021-06-10 20:23:14 CRI
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin ta bayyana wa kasar Japan rashin jin dadin ta, bisa yadda firaministan Japan Yoshihide Suga, ya kira yankin Taiwan da kasa mai cin gashin kai.
Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce kalaman na Mr. Suga, sun yi matukar keta alkawarin da Japan ta yi, na kin daukar Taiwan a matsayin kasa mai cin gashin kai.
Don haka Wang ya yi kira ga mahukuntan Japan, da su fayyace matsayarsu, tare da tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba a nan gaba. Ya kuma ja hankalin Japan da ta martaba alkawarin da ta yi, tare da yin taka tsantsan wajen furta kalamai, ko aiwatar da wani mataki da ka iya gurgunta matsayin kasar Sin, na kasancewa kasa mai cikakken ikon mulkin kai. (Saminu)
Labarai Masu Nasaba
- Yadda Amurka Take Goyon Bayan Shigar Yankin Taiwan Babban Taron WHO Ya Siyasantar Da Batun Kiwon Lafiya
- Babban taron WHO ya sake watsi da shawarar dake shafar Taiwan bisa ka’idar Sin daya kacal a duniya
- Majalisar kiwon lafiyar duniya ta yi watsi da batun dake shafar Taiwan
- Kasar Sin ta nanata adawarta da halartar yankin Taiwan babban taron hukumar lafiya ta duniya