logo

HAUSA

Za a shirya taron dandalin ilmin nazarin kasar Sin na duniya karo na 9 a Shanghai

2021-10-17 20:24:43 CRI

Daga ranakun 18 zuwa 19 ga watan nan na Oktoba za a gudanar da taron dandalin ilmin nazarin kasar Sin na duniya karo na 9 mai taken “Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Sin da kasashen duniya", taron zai gudana ne a cibiyar tarukan kasa da kasa dake Shanghai.

Ana sa ran taron dandalin zai gayyaci kwararrun masana 156 na cikin gida da wajen kasar Sin, wadanda za su tattauna game da tarihin jam’iyyar JKS da muhimmancinta game da makomar ci gaban kasar Sin da ma duniya a nan gaba daga fannoni daban daban, da suka hada da siyasa, tattalin arziki, zamantakewar al’umma da hulda tsakanin kasa da kasa.(Ahmad)

Ahmad