logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Cimma Manufarta Ta Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’ummar Kasa A Bana

2021-10-18 19:59:35 CRI

Yau ne, gwamnatin kasar Sin ta fitar da alkaluman tattalin arziki na rubu’i ukun farko a wannan shekara, inda jimillar GDPn kasar ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan 82313.1, wadda ta karu da kaso 9.8 cikin dari, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta daidaita mummunar barazana a wasu fannoni yadda ya kamata don bunkasa tattalin arzikinta, ta ci gaba da farfado da tattalin arzikinta. Saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin yana kan gaba a duniya.

A rubu’in ukun farkon bana, mutane miliyan 10.45 ne suka samu aikin yi a biranen kasar Sin, adadin da ya kai kaso 95 cikin dari bisa manufar da aka tsara a bana. Sa’an nan, karuwar kudin shigar mutane ta kusan yin daidai da karuwar tattalin arzikin kasar, wadda ta kai kaso 9.7 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara. Haka zalika, a rubu’in ukun farkon bana, jimillar kudaden da kasar Sin ta samu daga shigi da fice ta karu da kaso 22.7 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar bara, kana gudummawar da bangaren sayar da kaya da hidima zuwa ketare suka bayar ga ci gaban tattalin arzikin kasar ta kai kaso 19.5 cikin dari.

A matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, yadda kasar Sin ta yi ta farfado da tattalin arzikinta, yana da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tsarin samar da kaya da tsarin masana’antu na duniya. Tun farkon shekarar da muka ciki, zirga-zirgar jiragen ruwa a tashoshin jiragen ruwan kasar Sin da kuma kyawawan alkaluman cinikin waje dukkansu sun nuna farfadowar tattalin arzikin kasar Sin. Har ila yau, yadda kasuwar kasar Sin ta kara bude kofofinta ga ketare ta samar wa masu zuba jari na kasa da kasa kyakkyawar dama. Daga watan Janairu zuwa watan Agustan bana, yawan jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi a zahiri ya karu da kaso 22.3 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar bara, lamarin da ya nuna cewa, masu zuba jari na duniya sun nuna sha’awa da amincewa kan kasuwar kasar Sin. Sakamakon yadda kasar Sin ta zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, ya sa kasar Sin da ta kara bude kofa ga waje, za ta kara cin gajiyar bunkasar kanta tare da sauran kasashen duniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan