logo

HAUSA

Xi Ya Yi Kira A Bunkasa Aikin Nazarin Kayayyakin Tarihi Mai Sigar Musamman Ta Kasar Sin

2021-10-17 17:28:12 CRI

Xi Ya Yi Kira A Bunkasa Aikin Nazarin Kayayyakin Tarihi Mai Sigar Musamman Ta Kasar Sin_fororder_aladu

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a bunkasa aikin nazarin kayayyakin tarihi mai salo da sigar musamman ta kasar Sin.

Xi ya yi wannan tsokaci ne cikin wasikar taya murna da ya gabatar na bikin cika shekaru 100 da gano al’adun Yangshao, da kuma fara aikin nazarin kayayyakin tarihi na zamani a kasar Sin.

Sama da shekaru 100 da suka gabata, masana masu aikin nazarin kayayyakin tarihi sun cimma nasarori masu yawa ta hanyar yin aiki tukuru, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa wajen samun cikakkiyar fahimta kan wayewar kan al’ummar Sinawa mai dogon tarihi. Xi ya kara da cewa, wadannan abubuwan tarihin da aka gano sun kara haskaka muhimmiyar gudunmawar da wayewar kan al’ummar Sinawa ta samar ga duniya.

Gano al’adun Yangshao dake gundumar Mianchi a lardin Henan, ya fara ne a watan Oktoban shekarar 1921, wanda ya kafa dambar aikin nazarin kayayyakin tarihi na zamani na kasar Sin.(Ahmad)

Ahmad