logo

HAUSA

Za A Gudanar Da Zama Na 6 Na Kwamitin Kolin JKS Na 19 A Watan Nuwanba

2021-08-31 20:28:51 CRI

A yau ne taron hukumar siyasar kwamitin kolin JKS, ya yanke shawarar cewa, za a gudanar da zama na shida na kwamitin kolin JKS karo na 19 a watan Nuwanba a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Kuma Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, shi ne ya jagoranci taron na yau.

Bisa ajandar taron da aka gabatar a yau Talata, hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, za ta gabatar da rahoton aikin ga zaman, inda za a nazarta da bitar manyan nasarorin da ake cimma, da darasi na tarihi da aka koya, a shekaru 100 na gwagwarmayar JKS. (Ibrahim)

Ibrahim