logo

HAUSA

An Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Kan Akidu Tsakanin Jam’iyyun Kasashen Sin Da Afirka Karo Na 4

2021-09-25 17:37:12 CRI

Ranar 24 ga wata, an gudanar da taron kara wa juna sani kan akidu tsakanin jam’iyyun kasashen Sin da Afirka karo na 4 ta kafar bidiyo, inda shugabannin jam’iyyu da jami’an jam’iyyu kusan dari 3 daga kasashe 14 na Afirka suka halarta.

A cikin jawabinsa, Song Tao, shugaban sashen kula da cudanya da kasashen waje na kwamitin tsakiya na JKS, ya yi karin bayani kan tarihi da kyawawan fasahohin da kwamitin tsakiyar jam’iyyar dake karkashin shugabancin Xi Jinping, ya samu wajen jagorantar jama’ar Sin a fagen neman samun hanyar gurguzu mai halin musamamn na kasar Sin cikin shekaru 100 bayan kafuwar jam’iyyar, musamman ma bayan babban taron wakilan JKS karo na 18. Song ya nuna cewa, muhimmin dalilin da ya sa hanyar gurguzu mai halin musamman na kasar Sin ta samu nasara shi ne, jagorancin JKS. Ya ce yadda JKS ta kafa hanyar zamanintar da kasa mai salon kasar Sin, ta fadada hanyoyin raya kasashe masu tasowa na zamani. JKS tana son hada kai da jam’iyyun kasashen Afirka wajen ingantar mu’amala da koyi da juna a fannin kyawawan fasahohin tafiyar da harkokin kasa, a kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga kasashen Sin da Afirka.

A nasu bangaren, shugabannin jam’iyyun kasashen Afirka sun ce, kyawawan fasahohin kasar Sin sun zama abin koyi ga jam’iyyun kasashen Afirka, tare da karfafa gwiwarsu wajen bin wata hanyar raya kasa da ta dace da yanayin kasashensu. Sun ce suna son inganta mu’amala da hadin gwiwa da JKS wajen kara ciyar da huldar da ke tsakanin kasashen Afirka da Sin gaba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan