logo

HAUSA

Xi Ya Yi Kira Ga Matasa Jami’ai Da Su Kasance Masu Biyayya Cancanta Kan Muhimman Ayyuka

2021-09-01 21:35:51 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga matasa jami’ai, da su tsaya kan burinsu, da yin biyayya ga jami’yyar Kwaminis ta kasar Sin, da neman gaskiya daga shaidu, su kuma sauke nauyin da aka damka musu, su kuma nace wajen zama kashin bayan al’umma, wadanda jam’iyyar da jama’a suka amince da su kan muhimman ayyuka.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kwamitin kolin aikin soja, ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi a yayin zaman horaswa da aka shiryawa matasa da matsakaitan jami’ai a makarantar kwamitin kolin JKS.

Xi ya bayyana cewa, har kullum JKS, ta kasance jami’iyyar dake da kyawawan manufofi da tabbatacciyar hujja. Yana mai cewa, wannan akida da manufofi, suna nufin imani da ra’ayin Markisanci, babban burin Kwaminisanci da burin gurguzu mai sigar kasar Sin.

Ya kara da cewa, duk mai irin wadannan manufofi da yakini ne kawai ke iya zama mamban JKS da ma jami’ai, wadanda za su iya jure gwaje-gwaje, har su iya yin tafiya mai nisa.

Da yake jaddada hanyar kaiwa ga mafita, Xi ya bukaci matasa jami’ai da su ziyarci sassa daban daban na kasar, don koyon ci gaban da aka samu da kuma rauni, yayin da ake yabawa ko sukar su, ta yadda za su kara fahimtar hakikanin halin da ake ciki,

Xi ya ce, riko da ka’idoji, su ne muhimman halayen ‘yan kwaminis, kuma muhimman ma’auni na kimanta kwarewar jami’ai. Ya kara da cewa, ya kamata dukkan jami’an JKS, su kasance masu adalci, wajen gudanar da ayyuka, ba tare nuna son kai yayin gudanar da ayyukansa ba.(Ibrahim)

Ibrahim