logo

HAUSA

Burin JKS Shi Ne Bayar Da Nata Gudummowa Ga Duniya

2021-08-29 16:49:42 CRI

Kwanan baya, sashen yada labarai na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin JKS ya wallafa wata takarda mai taken “Nauyin da JKS ta dauka da kuma gudummawar da ta bayar”, inda ya nuna cewa, JKS na da babban burin bayar da nata gudummowa ga duniya, a maimakon yin kama karya ga duniya, lamarin da ya burge duniya sosai. Wannan ba wai bayani ne kawai da jam’iyyar ta yi ba, wannan shi ne yadda jam’iyyar mai tarihin shekaru 100 da kafuwa mafi girma a duniya take gwagwarmayarta.

A shekarun 1950, kasar Sin ta gabatar da ka’idoji 5 na yin zaman tare cikin ruwan sanyi dangane da raya hulda a tsakanin kasa da kasa, sa’an nan bayan da ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare, ta dora muhimmanci kan batutuwan zaman lafiya da ci gaba a zamanin yanzu. Daga bisani kuma ta gabatar da wasu muhimman tunani da shawarwari, alal misali, raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam da kuma kafa sabuwar hulda a tsakanin kasa da kasa. Har kullum gwamnatin kasar Sin da ke karkashin shugabancin JKS tana bayar da dabaru da basira wajen kiyaye zaman lafiya a duniya.

Sanin kowa na cewa, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, kasar Sin ba ta taba ta da wani yaki ko hargitsi ba. Ba ta kutsa kai cikin wata kasa ba. A maimakon haka, yanzu kasar Sin ta zama ta biyu a duniya wajen ba da kudi kan ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, kana kuma ita ce wadda ta fi tura sojojin kiyaye zaman lafiya da yawa cikin dukkan kasashen da ke da kujerar din din din a MDD. Har ila yau kasar Sin ta shiga ayyukan yin kwaskwarima da kyautata tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa, tana kuma yin kokari ba tare da kasala ba wajen rage talauci da yaki da ta’addanci a duniya.

Bayan haka kuma, JKS tana kara azama wajen samun ci gaba tare. A wani bangare kuma, JKS tana jagorantar kasa mai tasowa mafi girma a duniya wajen raya kasa ta zamani, lamarin da ya ba da gudummowa wajen ci gaban duniya. A wani bangare na daban kuma, kasar Sin tana kara azama kan ci gaban kasashen duniya baki daya ta hanyar raya kanta yadda ya kamata.

Abin da ya dace a lura shi ne, shawarar kasar Sin ta “ziri daya da hanya daya” ta kasance wani muhimmin dandali ta fuskar samun ci gaba tare. Abu mai muhimmanci shi ne, yayin da ake fuskantar manyan sauye-sauye, JKS ta gabatar da tunanin “raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam”, lamarin da ya kafa wata sabuwar hanyar raya kasa.

Tarihin JKS ya shaida mana cewa, wannan jam’iyya mafi girma a duniya wadda take jagorantar kasar Sin tana da babban burinta, tana kokarin kawo wa jama’ar Sin alheri, tare kuma da kara azama kan ci gaban ‘yan Adam baki daya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan