logo

HAUSA

WHO: karancin alluran riga kafi ka iya kawo tsaiko ga burin Afrika na yi wa kaso 40 cikin dari na al’ummarta riga kafi

2021-09-17 10:28:59 CRI

WHO: karancin alluran riga kafi ka iya kawo tsaiko ga burin Afrika na yi wa kaso 40 cikin dari na al’ummarta riga kafi_fororder_210917-fa'iza-2-vaccination

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce burin nahiyar Afrika na yi wa kaso 40 cikin dari na al’ummarta riga kafin COVID-19 zuwa watan Disamban bana, na fuskantar kalubale biyo bayan karancin samar da alluran daga bangarori daban-daban.

Daraktar hukumar a nahiyar Afrika Matshidiso Moeti, ta ce yanzu nahiyar na fuskantar karancin allurai kusan miliyan 500, yayin da shirin COVAX ya rage allurai miliyan 150 da aka tsara samarwa a bana. 

A cewarta, allurai miliyan 470 ne kadai COVAX zai samarwa nahiyar a bana, wanda zai ishi kaso 17 cikin dari na al’ummarta, abun da ta ce zai kawo nakasu ga kokarin da ake na kara yawan mutanen da suka samu riga kafin. (Fa’iza Mustapha)