logo

HAUSA

WHO tana fatan yiwa kashi 10 bisa 100 na ‘yan Afrika rigakafi zuwa karshen Satumba

2021-08-27 10:02:59 CRI

WHO tana fatan yiwa kashi 10 bisa 100 na ‘yan Afrika rigakafi zuwa karshen Satumba_fororder_WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce tana fatan za a yiwa kashi 10 bisa 100 na mutanen Afrika rigakafin COVID-19 nan da karshen watan Satumba, jami’in WHO na shiyyar Afrika ya bayyana hakan, inda ya bukaci a karfafa hadin gwiwar aikin riga-kafin cutar ta COVID-19.

Matshidiso Moeti, daraktar hukumar WHO a shiyyar Afrika, ta ce ana sa ran samun alluran rigakafin guda miliyan 117 nan da wata mai kamawa, kuma ana bukatar karin wasu alluran miliyan 34 domin cimma wannan buri. Ofishin hukumar WHO na shiyyar Afrika yana Brazzaville, babban birnin jamhuriyar Kongo.

A cewar WHO, tun bayan barkewar annobar COVID-19, adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 7.6, yayin da aka samu hasarar rayuka sama da 191,000.

Ko da yake zagaye na uku na barkewar cutar COVID-19 ya daidaita, amma har yanzu nahiyar ba ta kubuta daga barazanar annobar ba, kasancewar an samu adadin masu kamuwa da cutar kusan 248,000 a makon da ya gabata, kamar yadda Moeti ta yi gargadi.

Ga Afrika, burin da ake da shi shi ne, a yiwa a kalla kashi 20 bisa 100 na yawan al’ummar rigakafin ta hanyar samar da allurai miliyan 600 nan da karshen shekarar 2021, a cewar hukumar ta WHO.(Ahmad)