logo

HAUSA

Kasar ta fidda bayanan tarihin hadin gwiwar kasa da kasa game da binciken hukumar WHO game da asalin cutar SARS-CoV-2

2021-09-30 16:10:39 CRI

Kasar ta fidda bayanan tarihin hadin gwiwar kasa da kasa game da binciken hukumar WHO game da asalin cutar SARS-CoV-2_fororder_210930-Ahmad 3

A ranar Laraba kasar Sin ta fidda bayanan hadin gwiwar kasa da kasa game da binciken da huumar lafiya ta duniya WHO ta jagoranta game da tushen annobar cutar mashako ta SARS-CoV-2.

Bayanan sun nuna cewa, binciken asalin cutar lamari ne mai sarkakiya kuma batu ne da ya shafi kimiyya. Domin nazarin asalin cutar, da yadda take yaduwa da kuma yadda annobar COVID-19 ta barke, wadda ta bazu a kasashen duniya sama da 200 da shiyyoyi, masana kimiyya na kasashen duniya na bukatar yin aiki tare domin baiwa fannin kimiyya dama, da goyon baya da kuma hadin gwiwa domin kaucewa daukar matakai bisa jahilci, da nuna wariya da rashin adalci.

Kasar Sin tana sauke nauyin dake bisa wuyanta game da aikin kandagarkin annobar COVID-19 da kuma dakile annobar. Haka zalika, sau biyu kasar ta gayyato kwararrun kasa da kasa domin su gudanar da aikin binciken asalin annobar. A bisa matakai na kimiyya, da bude kofa, da yin hadin gwiwar ba tare da rufa-rufa ba, kasar Sin ta bayar da dukkan damammaki ga tawagar kwararrun masana na hukumar WHO a lokacin da suka gudanar da aikinsu a Wuhan. Domin sauke nauyi da kuma bukatar gaggawa, tawagar hadin gwiwa na kwararrun hukumar WHO da kasar Sin sun kammala ayyukansu na nazarin binciken asalin cutar, inda suka bayar da bayanan hakikanin yadda matakan da suka bi wajen gudanar da ayyukansu da kuma manyan sakamakon da suka samu game da binciken asalin annobar gami da shawarwarin da suka bayar domin bin matakai na gaba na aikin binciken asalin cutar a duniya. (Ahmad)