Kwararrun WHO: Babu alkaluman da za su shaida ra’ayin samun bazuwar kwayar cutar COVID-19 daga dakin gwaji
2021-08-27 10:47:10 CMG
A cikin mujallar “Nature” da aka buga a kasar Birtaniya a jiya Alhamis, wasu kwararru fiye da 10 na hukumar lafiya ta duniya WHO sun gabatar da wani bayani cewa, tun bayan da aka gabatar da rahoton aikin binciken asalin cutar COVID-19 da kasar Sin da hukumar WHO suka gudanar cikin hadin gwiwa, an yi kira ga kasashe daban daban da su mika wa WHO duk wasu alkaluman da za su shaida ra’ayin samun bazuwar kwayar cutar COVID-19 daga wani dakin gwaji. Sai dai har yanzu, ba a samu ko guda daya ba.
A farkon bana, wasu kwararru 17 na kasar Sin, da takwarorinsu 17 na kasashen waje, sun kafa wata kungiyar hadin gwiwa, don gudanar da aikin binciken gano asalin cutar COVID-19 da ya shafi kasar Sin a birnin Wuhan na kasar, cikin wasu kwanaki 28. Kana sun gabatar da rahoton bincikensu a watan Maris na bana, inda suka ce “kusan ba zai yiwu ba” a samu bazuwar kwayoyin cutar COVID-19 daga wani dakin gwaji, kana yana da muhimmanci a yi bincike kan yadda kwayar cutar ta fara yaduwa a sauran kasashe. Ban da haka, sun gabatar da wasu shawarwari game da yadda za a gudanar da aikin binciken gano asalin cutar COVID-19 a nan gaba.
An jaddada a cikin bayanin cewa, aikin binciken gano asalin cutar COVID-19, aiki ne da aka ba shi fifiko sosai, kana ana gudanar da shi bisa tushen kimiyya da fasaha. An ce aikin na cikin wani lokaci mai muhimmanci, ganin yadda aka fara rasa damar gudanar da wasu bincike a kasashe daban daban. Haka zalika, an nuna wasu ayyukan da ya kamata a fara gudanar da su yanzu, ciki har da neman mutanen da suka fara kamuwa da cutar COVID-19 a wurare daban daban na duniya. (Bello Wang)