logo

HAUSA

An yi bikin murnar ranar yawon shakatawa ta duniya a kasar Cote d’Ivoire

2021-09-29 13:45:42 CRI

A ranar 27 ga wata ne, aka kaddamar da bikin murnar ranar yawon shakatawa ta duniya karo na 41 a Abidjan, hedkwatar mulkin kasar Cote d’Ivoire, bisa babban taken “Yadda sha’anin yawon shakatawa ya sa kaimi ga samun ci gaba daga dukkan fannoni”.

A jawabinsa babban sakataren MDD António Guterres, ya yi kira da a sake yin tunani da ma yin gyare-gyare domin a farfado da sha’anin yawon shakata cikin tsaro.

Alkaluman kididdiya na nuna cewa, annobar cutar COVID-19 ta kawo cikas sosai ga sha’anin yawon shakatawa. Yawan mutanen da suka je yawon bude ido a ketare, ya ragu da kaso 75 cikin dari a shekarar 2020, lamarin da ya sa mutane miliyan 62 rasa guraben ayyukan yi. Ana hasashen cewa, ya zuwa karshen shekarar 2021, duniya za ta yi hasarar jimillar kudin GDP da ya kai dala triliyan 4.

Firaministan kasar Cote d’Ivoire Patrick Achi Jérôme ya sanar da cewa, ana kokarin raya kasarsa zuwa wurin yawon shakatawa mafi shahara na biyar a nahiyar Afirka. Ana sa ran masu bude ido miliyan 5 za su ziyarci kasar ya zuwa shekarar 2025, yayin da za a samar da guraban ayyukan yi dubu 750. (Kande Gao)

Kande Gao