logo

HAUSA

Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afrika ya kusan kai miliyan 8.04

2021-09-14 09:40:03 CMG

Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afrika ya kusan kai miliyan 8.04_fororder_fa'iza-2-Afirka-COVID-19

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC, ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika, ya kai 8,039,647 zuwa yammcin jiya Litinin.

A cewar cibiyar, Afrika ta Kudu da Morocco da Tunisia da Habasha na daga cikin kasashen da suka fi fama da cutar.

A bangaren yawan adadin masu cutar, yankin kudanci nahiyar ne ke kan gaba, sai arewaci sai kuma yankin gabashi, yayin da yankin tsakiyar nahiyar ke da adadi mafi karanci. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza