logo

HAUSA

Gudummawar Riga-kafin COVID-19 Da Sin Ta Samar Sun Isa Burkina Faso

2021-09-20 16:19:43 CRI

Da yammacin ranar 18 ga watan Satumba, alluran riga-kafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta bayar da gudummawa sun isa filin jirgin saman kasa da kasa na Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso. Jakadan kasar Sin a Burkina Faso Li Jian, da wakilan ma’aikatar harkokin wajen kasar Burkina Faso, da jami’an hukumar lafiya ta duniya WHO, sun halarci bikin mika riga-kafin.

Jakada Li Jian ya bayyana a wajen bikin cewa, kasar Sin ta samar da gudummawar alluran riga-kafin COVID-19 kimanin 400,000, hakan wasu alamu ne dake kara bayyana kyakkyawar huldar dake tsakanin kasashen biyu. Sannan matakin ya bayyana kyakkyawar aminta dake tsakanin al’ummun kasashen biyu, kana lamarin ya nuna cewa, kasashen biyu suna goyon bayan junansu a lokacin da ake fuskantar wahalhalu. Li ya kara da cewa, an yi amanna cewa, gudummawar riga-kafin za su taimakawa kasar Burkina Faso a yaki da annobar da kuma kare lafiyar al’ummar kasar.

Clarisse Merindol Ouoba, ministar mai wakiltar ma’aikatar harkokin wajen Burkina Faso, ta bayyana godiya ga gwamnatin Sin bisa taimakon riga-kafin da ta baiwa kasarta. Ouoba ta ce, a halin yanzu an samu nasarar dakile annobar, sakamakon babban taimakon da Sin ta baiwa kasar. (Ahmad)

Ahmad