logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar COVID-19 a Amurka ya zarce na murar Flu na shekarar 1918

2021-09-21 16:00:25 CRI

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Amurka, ya zarce 675,000, wanda aka yi kiyasin annobar murar Flu ta yi sanadinsu a shekarar 1918.

Bisa alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta fitar, zuwa karfe 4:21 da yamma jiya Litinin agogon gabashin kasar, Amurkawa 675,446 ne suka mutu sanadiyyar cutar COVID-19, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar ya zarce miliyan 42.

Ana ganin akwai yuwuwar ci gaba da karuwar adadin mamatan yayin da kasar ta shiga wani sabon zagayen barkewar sabon nau’in cutar na Delta.

Tom Frieden, tsohon shugaban cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta kasar wato CDC ya wallafa a shafin Tweeter cewa, “addain wadanda aka bayar da rahoton mutuwarsu sanadiyyar cutar COVID-19 zai zarce adadin na murar flu a shekarar 1918 a wannan watan. Bai kamata mu saduda da ci gaban annobar da za a iya kandagarkinta ba.”

Cibiyar CDC ta Amurka, ta yi kiyasin a shekarar 1918, murar flu ta yi sanadin mutuwar Amurkawa 675,000. Har kawo yanzu, ana ganin annobar a matsayin mafi muni a tarihin Amurka. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha