logo

HAUSA

Kasar Sin za ta bada gudunmuwar alluran riga kafin COVID-19 ga Afghanistan

2021-09-14 09:38:42 CMG

Kasar Sin za ta bada gudunmuwar alluran riga kafin COVID-19 ga Afghanistan_fororder_fa'iza-1-Afghanistan-Sin

Kasar Sin za ta bayar da gudunmuwar alluran riga kafin COVID-19 miliyan 3 ga Afghanistan a kashin farko, inda za ta bayar da karin wasu daga baya.

Chen Xu, shugaban tawagar Sin a ofishin MDD dake Geneva ne ya bayyana hakan, inda ya ce Kasar Sin ta yanke shawarar gaggauta samar da abinci da kayayyakin sanyi da riga kafin COVID-19 da magungunan da darajarsu ta kai yuan miliyan 200 ga Afghanistan

A cewarsa, Kasar Sin na girmama cikakken ‘yanci da yankin Afghanistan a matsayinta na makwabciyarta, kana ta nacewa ga kaucewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe da bin manufar abota, yayin da take hulda da al’ummar Afghanistan. (Fa’iza Mustapha)

Bello