logo

HAUSA

Rigakafin COVID-19 Da Kasar Sin Ta Ba Da Gudummowa A Rukuni Na 4 Ya Isa Harare

2021-09-27 11:39:38 CRI

Rigakafin COVID-19 Da Kasar Sin Ta Ba Da Gudummowa A Rukuni Na 4 Ya Isa Harare_fororder_zimbabwe

Da yammacin ranar 26 ga wata, wani jirgin sama dauke da alluran rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 na kamfanin SINOPHARM na kasar Sin ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Robert Mugabe a birnin Harare, hedkwatar kasar Zimbabwe, wanda shi ne rukuni na 4 na gudummawar kasar Sin ga Zimbabwe. Constantino Chiwenga, mataimakin shugaban Zimbabwe, kana ministan lafiyar kasar ya yi maraba da rigakafin tare da karbar su a madadin gwamnatinsa.

A filin jirgin saman, Chiwenga ya nuna godiya ga yadda kasar Sin take taimakawa Zimbabwe wajen yaki da annobar, inda ya ce, Sin ta rika bai wa Zimbabwe taimako wajen yaki da annobar, lamarin da ya nuna dankon zumuncin dake tsakanin kasashen 2. Bayan barkewar annobar a Zimbabwe a ranar 30 ga watan Maris na bara, kasar Sin ta ba da taimakon fasaha da kayayyaki da goyon baya matuka, wadanda suka inganta karfin Zimbabwe na yaki da annobar. Gwamnatin Zimbabwe tana gode wa gwamnatin Sin bisa taimakon da take bayarwa wajen ba al’ummar Zimbabwe kariya daga kamuwa da annobar.

Chiwenga ya kara da cewa, yanzu akwai rashin daidaito a fannin rabon rigakafin a duniya. Amma sakamakon samun rigakafin kasar Sin kan lokaci, ana yi wa a’ummar Zimbabwe allurar yadda ya kamata. Yanzu yawan mutanen da aka yi wa allurar bisa jimillar mutanen kasar Zimbabwe, ya kai matsayi na 7 a cikin kasashe 54 na Afirka.

Alkaluman ma’aikatar lafiyar Zimbabwe sun nuna cewa, ya zuwa ranar 25 ga wata, a cikin dukkan mutanen kasar miliyan 14, an yi wa wasu miliyan 3 da dubu 30 allurar a kalla sau 1, daga cikinsu kuma an yi wa miliyan 2 da dubu 180 allurar sau 2. An yi wa yawancin wadannan mutanen ne allurar kasar Sin. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan