logo

HAUSA

Zimbabwe Ta Karbi Kashi Na 3 Na Riga-kafin COVID-19 Daga Kasar Sin

2021-03-31 10:42:58 CRI

A jiya Talata kasar Zimbabwe ta karbi kashi na uku na alluran riga-kafin cutar COVID-19 daga kamfanin hada magunguna na Sinovac na kasar Sin.

Rukunin alluran na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke kokarin fadada aiwatar da shirinta na riga-kafin na kasa baki daya inda Zimbabwe ta sha alwashin yi wa ‘yan kasar akalla miliyan 10 riga-kafin.

Kawo yanzu, kasar Zimbabwe ta amince da yin amfani da riga-kafin COVID-19 guda hudu da suka hada da na kamfanonin Sinopharm da  Sinovac na kasar Sin, sai Sputnik V na kasar Rasha, da kuma Covaxin na kasar Indiya.

Kawo yanzu, an yi wa mutane kusan 70,000 riga-kafin kadai na kamfanin Sinopharm ko kuma na Sinovac daga kasar Sin.

Wannan kasar da ke kudancin Afrika tana burin yi wa kaso 60 na al’ummarta riga-kafin cutar COVID-19 domin jama’a su samu garkuwa.(Ahmad)

Ahmad