logo

HAUSA

Wata nas ‘yar kasar Sin dake taimakawa kokarin dakile cutar COVID-19 a kasar Zimbabwe

2021-05-13 13:41:42 CRI

Wata nas ‘yar kasar Sin dake taimakawa kokarin dakile cutar COVID-19 a kasar Zimbabwe_fororder_20210513-zimbabwe-bello.JPG

A asibitin da aka kebe domin kula da mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 dake kasar Zimbabwe, akwai wata nas ‘yar kasar Sin, wadda ke kokarin taimakawa dakile cutar a kasar.

Fu Yan, wata nas ce ‘yar kasar Sin, wadda ke aiki a asibitin Upper East Medical Center na kasar Zimbabwe, da aka kebe shi musamman domin jinyar mutanen da suka kamu da cutar COVID-19. Fu ta taba shiga aikin taimakawa lardin Hubei na kasar Sin wajen dakile annobar COVID-19 a farkon shekarar 2020, inda ta samu kwarewa a fannin kula da majiyyatan da suka kamu da cutar. Saboda haka aka gayyace ta don ta je kasar Zimbabwe a watan Nuwamban shekarar 2020, musamman ma domin ta taimakawa Sinawan da suke zama a kasar wajen tinkarar annobar COVID-19. Fu ta ce,

“Aikin da nake yi a nan shi ne taimakawa majiyyata Sinawa yin mu’amala da ma’aikatan lafiya. Wasu daga cikin majiyyatan suna fuskantar matsalar bambancin yare, don haka suna bukatar taimako. Wasunsu ba su da iyali a nan, don haka suna kallona a matsayin ‘yar uwarsu. Na kan shiga dakunansu a kowace rana, don bayyana musu yanayin da jikinsu ke ciki, da sakamakon binciken da aka yi, da wayar musu da kai dangane da cutar COVID-19, ta yadda ba za su ji tsoro sosai ba. ”

A farkon bana, yanayin annobar COVID-19 a kasar Zimbabwe ya sake tsananta, lamarin da ya sanya Fu Yan shan aiki sosai, saboda ita ce nas ‘yar kasar Sin daya tilo a kasar Zimbabwe. Ta taba samar da hidima ga majiyyata Sinawa fiye da 70 a lokaci guda.

Ban da kula da majiyyata a cikin asibiti, tana kuma kula da aikin amsa wayar da aka buga ma hukumar ba da taimakon gaggawa ga marasa lafiya, don ba da shawara ga Sinawan da suka gamu da matsalar lafiya, da kuma taimaka musu samun jinya a asibitoci. Wani likita dan kasar Zimbabwe mai suna Ali ya bayyana ra’ayinsa game da Fu Yan, inda ya ce,

“Na fara aiki tare da Fu Yan tun daga karshen bara. Tana da hikima, ta san ilimin aikin jinya sosai, kana tana kulawa da majiyyata, da nuna musu kauna. Halayyarta ta kirki ta sa ta zama wata nagartacciyar nas. Kullum ta kan gaya mana sabon yanayin da majiyyatan suke ciki, wannan yana da muhimmanci sosai ga aikin jinya da muke yi. Saboda wannan kulawar da ta yi, majiyyata suna warkewa cikin sauri. Ko da yake mu kan gamu da matsalar yare yayin da muke son mu’amala da wasu majiyyata, amma bisa taimakon da Fu ta bayar, mun samu sauki matuka. Muna girmama ta sosai.”

A farkon watan Maris na bana, bisa taimakon gidan jakadancin kasar Sin dake Zimbabwe, asibitin Upper East Medical Center da Fu take aiki ya kaddamar da wani aiki na yi wa Sinawa dake Zimbabwe allurar riga kafin cutar COVID-19. Fu ma ta halarci wannan aiki. A cewarta,

“Da farko dai mun kaddamar da aikin yin allurar riga kafi a Harare. Mun tsara wata manhaja don bayyana bukatar karbar allurar, inda musamman ma a mako na farko, mutanen da suke so a yi musu allura suka cika yawa. Asibitinmu ya taimakawa Sinawa 2000 karbar allurar a birnin Harare. Daga baya mun je sauran birane, don ci gaba da bayar da hidima.”

Fu Yan tana da hakuri da jajircewa, lamarin da ya sa take iya aiki a wata kasa ta daban ita kadai, gami da daukar nauyin ayyuka masu wahala. A cewarta, saboda ita ce nas ‘yar kasar Sin daya tak da ake iya samu cikin asibitin da take aiki, dukkan majiyyata Sinawa suna son neman taimakonta. Abin da ya sa take fuskantar dimbin ayyuka a cikin asibitin. Kana da ma Fu nas ce mai kula da majiyyata masu fama da ciwon zuciya. Sai dai bayan da ta je kasar Zimbabwe, ta fara kula da majiyyatan da suka gamu da matsaloli daban daban. Wannan ya tilasta ta koyon karin ilimi a fannin aikin jinya.

Ko da yake ayyukan suna da wahala, amma Fu tana jin dadi, ganin yadda ta iya taimakawa mutane masu bukata, da kare lafiyarsu. (Bello Wang)

Bello