logo

HAUSA

Zimbabwe za ta karfafa matakan yaki da COVID-19 yayin da cutar ke karuwa

2021-06-13 16:55:56 CMG

Zimbabwe za ta karfafa matakan yaki da COVID-19 yayin da cutar ke karuwa_fororder_0613-Zimbabwe-ahmad

Kasar Zimbabwe ta yanke kudirin karfafa matakan yaki da COVID-19 tun daga ranar Litinin mai zuwa, inda aka haramta dukkan tarukan jama’a da kuma tilasta yin gwaji ga dukkan matafiyan da suka shiga kasar daga kasashen da ake fama da yaduwar cutar, bayan da aka samu karuwar masu kamuwa da kuma masu mutuwa a sanadiyyar cutar cikin makonnin baya bayan nan.

Mataimakin shugaban kasar, kana ministan lafiyar kasar, Constantino Chiwenga, ya ce an samu sabbin masu kamuwa da cutar kimanin 596 a cikin kwanaki bakwai da suka gabata kana mutane 26 cutar ta kashe idan an kwatanta da makamancin lokacin a watan Mayun 2021 inda aka samu sabbin mutanen 132 da suka kamu da cutar sannan mutane 6 sun mutu. A cewar mataimakin shugaban kasar, adadin sabbin masu kamuwa da cutar da kuma wadanda suka mutu ya ninka sama da sau uku.

Ya kara cewa, abin bakin ciki ne, yadda mutane suke ta korafi wajen kiyaye matakan kariya daga cutar a unguwanni da wuraren ayyuka. Sannan ya ce, ana kara samun karuwar masu kamuwa da cutar da masu mutuwa a duniya da kuma yankunan kudancin Afrika SADC.

Chiwenga ya ce, za a dauki tsauraran matakan kariya, kamar wajabta amfanin da takunkumin rufe fuska, da bada tazara, da wanke hannu ko kuma amfani da sinadarin kashe cuta na sanitiza akai akai.(Ahmad)

Ahmad