logo

HAUSA

Shugaban kasar Zimbabwe Ya Gode Da Taimakon Da Kasar Sin Ta Samarwa Kasarsa Wajen Yakar COVID-19

2021-04-19 11:45:37 CRI

Shugaban kasar Zimbabwe Ya Gode Da Taimakon Da Kasar Sin Ta Samarwa Kasarsa Wajen Yakar COVID-19_fororder_xin

Kasar Zimbabwe ta yi murnar cika shekaru 41 da samun ’yancin kanta a ranar 18 ga wata.

An gudanar da bukukuwan murnar a fadar shugaban kasar a wannan rana. Sakamakon yaki da annobar COVID-19, an watsa bukukuwan ta shirin telibijin ga duk fadin kasar, a maimakon gayyatar mutane su kalla a fadar shugaban.

A cikin jawabinsa a yayin bikin, shugaba Emmerson Mnangagwa, ya godewa kasar Sin da sauran kasashen da ke kulla kyakkyawar hulda da Zimbabwe bisa kayayyaki da alluran rigakafin cutar COVID-19 da suke baiwa kasar. A cewar shugaban, taimakon ya taka muhimmiyar rawar da ba za a iya maye gurbinsa ba wajen taimakawa Zimbabwe yaki da annobar da farfado da tattalin arzikinta.

Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta aike da rukunoni 2 na alluran rigakafin kamfanin Sinopharm ga Zimbabwe. Sa’an nan gwamnatin Zimbabwe ta sayi alluran na kamfanin SINOVAC na kasar Sin har rukunoni 2. A cewar Shugaba Mnangagwa, sakamakon taimakon Sin da alluran, ya sa kasarsa ta gudanar da aikin yi wa al’umma allura yadda ya kamata. Yawan mutanen da aka yi musu alluran ya kai matsayi na 3 cikin kasashe mambobin kungiyar SADC, kana ya kai matsayi na 8 cikin dukkan kasashen Afirka. Ya zuwa ranar 17 ga wata, an yi wa mutane dubu 276 alluran a Zimbabwe baki daya. (Tasallah)

Tasallah Yuan