logo

HAUSA

AU ta bukaci masu ruwa da tsaki a Chadi su daidaita rikicin siyasar kasar cikin lumana

2021-08-29 16:32:09 CRI

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta bukaci masu ruwa da tsaki a kasar Chadi da su lalubo bakin zaren warware dambarwar siyasar kasar cikin lumana, kasancewar babu wani matakin soji da zai iya warware kalubalolin da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Sanarwar wadda kwamitin wanzar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55 ta fitar a ranar Juma’a, biyo bayan tattaunawar baya-bayan nan da kwamitin ya gudanar, inda ya nazarci ci gaban da aka samu game da shirin warware rikicin siyasar kasar Chadi da irin tallafin da AU ke bayarwa wajen cimma nasarar shirin.

Kwamitin ya sake jaddada yin kira ga bangaren gwamnatin rikon kwaryar kasar Chadi, da dukkan bangarorin masu ruwa da tsaki da suka hada da na jam’iyyun siyasa da kungiyoyin masu dauke da makamai da su amince da shiga tattaunawar sulhu ba tare da gindaya wasu sharruda ba.

Kwamitin ya kuma bukaci gwamnatin rikon kwaryar kasar da ta mutunta wa’adin watanni 18 da ta dauka domin kammala aikin mika mulki ga sabuwar gwamnati, kana ta jaddada cewa, dukkan mambobin kwamitin rikon kwarya na sojojin kasar ba su cancanci tsayawa takara neman shiga zaben kasar ba bayan kammala wa’adin gwamnatin rikon kwaryar kasar.(Ahmad)

Ahmad