logo

HAUSA

Jirgin saman Habasha ya yi fice a Afrika bayan jigilar riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 50

2021-09-05 16:46:03 CMG

Jirgin saman Habasha ya yi fice a Afrika bayan jigilar riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 50_fororder_0905-habasha-Ahmad

Kamfanin jiragen saman kasar Habasha ta gabashin Afrika wato Ethiopian Airlines, ya sanar a ranar Asabar cewa, ya yi jigilar alluran riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 50 zuwa kasashe 28 a fadin duniya.

Jirgin wanda ke dauke da wasu manyan fasahohin zamani da ake kira "Pharma Wing," ya yi nasarar jigilar alluran riga-kafin zuwa kasashe daban-daban, lamari da ya ba shi damar zama jirgin dake sahun gaba a fadin nahiyar Afrika wanda ya cimma wannan nasara.

A matsayinsa na kamfanin zirga-zirgar jirgin saman dake sahun gaba wajen yaki da COVID-19, kamfanin na Ethiopian Airlines ya yi jigilar muhimman kayayyakin kiwon lafiyar da aka fi tsananin bukata zuwa kasashen duniya sama da 80 tun bayan barkewar annobar, kamar yadda kamfanin ya sanar a ranar.

Sanarwar ta ce, a matsayinsa na kamfanin jirgin saman da bai taba katsewa zirga-zirgarsa ba a yayin da ake fama da dokar rufe kan iyakokin kasashe da dokar takaita zirga-zirga da kasashe ke kafawa sakamakon barkewar annoba, kamfanin jirgin saman yayi nasarar sada mutane sama da 63,000 da iyalansu daga kasashen duniya daban-daban.(Ahmad)

Ahmad